Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kai Farmaki a Kusa Da Damascus a Cewar Syria


Sojojin Syria sun ce Isra'ila ta harba makamai masu linzame a kusa da birnin Damascus har sojan Syria daya ya mutu.

Jiragen saman yakin Isra’ila sun harba makamai masu linzami a wasu wurare a kusa da birnin Damascus da safiyar ranar Laraba 30 ga watan Disamba, har wani sojan Syria ya mutu, wasu su 3 kuma suka jikkata, a cewar sojojin Syria.

Harin da aka kai bayan tsakar dare a yankin Zabadani da ke Damascus ya auna wurin da makaman kariyar Syria suke ne ya kuma lalata wasu wurare, abinda aka ji wani sojan Syria da ba a bayyana sunasa ba ya na fadawa kamfanin dillancin labaran SANA kenan.

Wannan shine hari na 2 da aka bada rahotonsa tun daga makon da ya gataba. Jiragen saman yakin Isra’ila sun tada bom a wasu wurare da ke tsakiyar garin Masyaf ranar Alhamis din da ta gabata.

Rahoton bai bada karin bayani ba kuma nan take Isra'ila ba ta ce komai ba, da ma da wuya Isra'ila ta bada rahoton hare-haren da ta ke kaiwa a cikin Syria a yakin basasar kasar da ake yi.

XS
SM
MD
LG