Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Israila Zata Cigaba da Kasancewa Kasar Yahudawa - Netanyahu


Firayim Ministan Israila Benjamen Ntanyahu
Firayim Ministan Israila Benjamen Ntanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yace, Isra’ila zata ga karshen bala’in sukar wuka kuma zata ci gaba da kasancewa kasarsu har abada.

Ya kara da cewa, “shekaru 100 na ta’addanci da neman rusa masu tsananin ra’ayin ganin dorewa kasar Yahudawa amma suna cigaba da rayuwa. Kuma har yanzu makiyanmu sun kasa yin karatun ta natsu.”

Mista Netanyahu yace abinda a kullum yake kaiwa ga nasara shine, yadda Yahudawa suka yarda da cewa Isra’ila kasarsu ce, sannansuna son su rayu a cikinta. Wadannan su ne nasararsu a kan makiyansu.

Ya kuma dora alhakin wadannan abubuwa akan Hamas da kungiyar ISIS wadanda suke anfani da karya da kiyayya da rikici don su kwace bangaren gabashin Jerusalem mai tsarki daga hannun Musulmi da Yahudawa.

Jita-jitar inda Musulmi ke kira da al-Aqsa su kuma Yahudawa kan kira wajen Tsaunin Bauta, shi ne dalilin yin duk wani rikici a wajen.

Netanyahu ya yi kira ga Larabawa ‘yan Isra’ila da su juyawa ta’addanci baya su rungumi zaman lafiya da lumana.

A wani labarin kuma, Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya fada jiya Litinin cewa, ‘yan kungiyar ISIS sune na farko da ake zargi da kai harin bakin wake kasarsa.

To saidai jami’an binciken kasar suna neman gano wadanda suke da alhakin harin kunar bakin waken birnin Ankara wanda ya hallaka mutane 97.

Davutoglu yace, jami’an binciken na gab da bayyana ‘yan kunar bakin waken da kuma bada shedar da zata tabbatar da wadanda ake zargin. Sannan an gane yadda ‘yan ta’addan suka isa wajen da suka aikata ta’asar.

Jaridar Turkiyya ta rawaito cewa, an debi jinin iyalan mutane goma sha shida da ake kyautata zaton ‘yan ISIS ne, don gwadasuda na ‘yan kunar bakin waken.

XS
SM
MD
LG