Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IZALA: Ta Musanta Kalamun Gwamnan Borno Kan Yin Wa'azi


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Kashim Shettima yayinda ya ziyarci wadanda kungiyar Boko Haram ta yiwa illa

Kungiyar IZALA ta musanta kamun da gwamnan Borno Ibrahim Shettima ya yi na cewa kungiyoyin addinin musulunci basa wa'azi akan illar irin kungiyoyi kamar Boko Haram

Kungiyar ta musanta batun cewa kungiyoyin musulunci basa wa'azi akan illolin kungiyar Boko Haram kamar yadda gwamnan jihar Borno Ibrahinm Shettima ya ambato..

Kungiyar tace wasu malaman addinin musulunci da suka hada da Shaikh Jaafar da Shaikh Albani duk an kashesu ne sabili da bayyana illolin da kungiyar Boko Haram ke haddasawa.

Dr Hassan Abubakar Dikko mai shugabancin shirya gasar karatun Qur'ani na kasa a karkashin kungiyar IZALA yace idan har gwamnan Borno yana ganin kungiyar ta gaza ta wannan hanyar to bibiyarsa ta addinin musulunci ce ta yi kadan domin tsarin kungiyar shi ne duk wata sai ta shirya wa'azi a kasa baki daya. Koina kungiyar na maganar illar Boko Haram har ma a jihohi.

A shekarar 2011 Shaikh Yahaya Jingir ya jagoranci malaman Najeriya gaba daya suka je Maiduguri suka yi wa'azi akan Boko Haram. Wa'azin da suke yi akan kungiyar Boko Haram yana cikin dalilin da ya sa wasu malaman suka rasa rayukansu. Shi kansa Shaikh Jingir an kai masa hari a masallacin 'yan taya a Jos domin yana wa'azi akan 'yan Boko Haram..

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG