Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagorar Myanmar Ta yi Allah Wadai Da Take Hakkin Bil'adama a Jihar Rakhine


Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, a wani lokaci da take jawabi a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya
Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, a wani lokaci da take jawabi a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya

Yayin da kasashen duniya suka kasa kunnuwansu domin jin jawabin jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi ta gabatar da jawabin nata a karon farko kan rikicin da ya tilastawa dubun dubatar Musulmi 'yan kabilar Rohingya ficewa daga kasar.

Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta ce gwamnatinta ta na Allah wadai da take hakkokin bil'adama da aka yi a yammacin jihar Rakhine, inda aka tilastawa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya kusan 400,000 suka fice zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da kasar.

A wani jawabi da ta yi a yau Talata a Naypyitaw, babban Birnin kasar a gaban wasu jami’an diplomisiyyar kasashen waje, jagorar, wacce ta taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya, ta ce kasar a shirye take ta ba da dama kasashen waje su je su yi bincike.

Ta kuma ba da tabbacin cewa za su binciki duk wani zargin take hakkin bil adama da aka yi a kasar.

Sai dai ta ce, za su dauki mataki ne akan zarge-zargen idan har aka samu kwararan hujjoji, tana mai cewa za su samar da wani tsari wanda zai bai wa mutanen da suka tsere su dawo gida bayan an tantance su.

Aung San Suu Kyi ta kuma ce duk da rikicin da aka samu, akwai Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya da dama da suke zaune a jihar ta Rakhine kuma babu abinda ya same su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG