Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijer Ta Cika Shekara 60 Da Samun 'Yancin Kai


Albarkacin zagayowar wannan rana, shugaban kasar Issouhou Mahamadou ya yi jawabi ga al’ummar kasar inda ya tabo wasu mahimman batutuwa da suka shafi sha’anin mulkin kasar a wannan lokaci da duniya ke fama da kalubale kala-kala.

Zabubukan da ake shirin gudanarwa a karshen shekarar nan ta 2020 na kan gaba a jerin batutuwan da shugaban kasar ya maida hankali akansu a jawabinsa na jajibirin sallar samun ‘yancin kai daga turawan Faransa.

Shugaba Issouhou Mahamadou ya ce "za mu gudanar da zabubukan nan bisa tsari kamar yadda muka yi alkawari."

Ya ce "cikar wannan guri shine aiki mafi muhimanci da zan yi alfahari da shi saboda na yi tsayin daka don ganin an shirya, kuma an gudanar da wadanan zabubbuka cikin kyakkyawan yanayi saboda yadda suke da mahimmanci ga tarihin wannan kasa."

Issouhou Mahamadou ya ce wannan ne karon farko tun sa'adda kasar ta sami 'yancin kai shekaru 60 da suka gabata, da zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya za ta mika mulki ga wata gwamnatin ta dimokaradiyya. "Wannan ne ya sa gwamnati ta dauki dukkan matakan da za su ba da damar gudanar da zabe cikin nasara, ta hanyar kafa sahihiyar hukumar zabe da amintaciyar kotun tsarin Mulki." Shugaban ya ce, ya gamsu da aiyukan rajistar da aka gudanar domin wadanan zabubbuka.

Akan maganar tsaro shugaban kasar ta Nijer ya ce "muna ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a wurare da dama. Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a tafkin Chadi da kungiyoyin ta’addanci da na tsaregun dake iyakokin kasarmu da kasashen Mali da Burkina Faso da ‘yan bindigar iyakar jihar Maradi da tarayyar Najeriya, da kuma masu safarar haramtattun abubuwa iri-iri a hamadar Sahara iyaka da Libya."

"Ya ce, yakin da mu ke gwabzawa da kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan tsagera wani abu ne da zai dauki lokaci sosai, saboda haka ya zama wajibi mu kara jan damara domin tabbatar da tsaron kasa mai fadi irin tamu, dole ne mu ninka yawan jami’an tsaronmu nan da shekaru biyu masu zuwa. Ya na da kyau kuma mu maida hankali akan wajen basu horo tare da samar da ingantatun kayan yaki."

A cewarsa koda yake amfani da karfin soja na iya bada damar murkushe ta’addanci ya zama wajibi a karfafa hanyoyin inganta fannin tattalin arziki da jin dadin rayuwar al’umma.

Nasarorin da Jamhuriyar Nijer ta samu wajen murkushe annobar coronavirus wani abu ne da Shugaban kasar Issouhou Mahamadou ya ce, ya na alfahari da shi, amma ya yi gargadin cewa dole a yi taka-tsantsan da wannan bala’i da ya addabi duniya baki daya.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG