Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ai A Amurka Sun Cafke Wasu Yan Damfara Har 61


Leslie Caldwell

Hukumomin shara’a na Amurka sun cafke wasu mutane 61 da akace suna cikin rukunin wasu mazambata dake yawan kiran mutane ta waya, suna tsorata su don su basu kudi, inda kuma akace izuwa yanzu sun firgita mutane kamar 15,000, kuma sun tatsi makurddan kudade sun fi Dala Milyan 300 daga wurinsu.

Jami’an ma’aikatar shara’a na Amurka sunce mutanen da aka kaman suna da alaka da wata cibiyar wayar tarho dake kasar India, wacce kuma ke da rassa kamar guda biyar dake warwatse a kasashen Amurka da India din.

Mataimakiyar Atone-Janar ta Amurka, Leslie Caldwell, tace galibi masu wayar sukan auna tsofaffin mutanen da suka yi ritaya daga aiki ne ko kuma bakin haure ne, inda suke tsorata su da cewa za’a zo a kama su ko a fitarda su daga Amurka muddin basu biya wasu mankudan kudade ba.

Ms Caldwell ta gayawa manema labarai cewa mutanen nan sunfi shekaru hudu suna gudanar da wannan ta’asar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG