Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Diflomasiyyar Rasha Da Aka Kora Na Shirin Barin London


Firaministar Burtaniya Theresa May

Tun bayan harin gubar da aka kai akan tsohon jami'in leken asirin Rasha Sergei Skripal a Burtaniyya, Rasha ta ce babu ruwanta.

Jami’an diflomasiyyar Rasha da kasar Burtaniyya ta bada umurnin a kore su daga bakin aiki saboda harin gubar da aka kai a kasar ta Burtaniyya na shirin barin kasar.

Kafafen yada labaran Rasha sun bada rahoton cewa an ga wata babbar motar kwasar kaya a wajen ofishin jakadancin Rasha dake birnin London yau Talata.

Kasar Burtaniyya dai ta bada umurnin a kori jami’an diflomasiyyar ne a makon da ya gabata, bayan da ta dorawa Rasha laifin kaiwa wani tsohon jami’in leken asirin Rasha, Sergei Skripal da diyarsa Yulia harin guba a garin Salsbury dake Burtaniyya a farkon watan nan.

Ita ma Rasha ta mayar da martani inda ta kori jami’an diplomasiyyar Burtaniyya 23, wadanda su ma ake sa-ran zasu bar birnin Moscow cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Rasha ta kuma musanta cewa tana da hannu a harin gubar da aka kai.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG