A makon jiya ne dai hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta sanar da cewa za ta kaddamar da bincike bayan da ta samu wani korafi da wasu mutane dake zargin cewa Majalisar ta kashe Naira Biliyan hudu zuwa shida ba bisa ka’ida ba, cikin shekaru uku.
Jami’an kula da harkokin kudi na majalisar masarautar Kano dai sun bayyana a hedikwatar hukumar yaki da rashawa, a cewar Kwamrad Muhiyi Magaji, shugaban hukumar ta Kano, ya ce sun tattauna da ‘yan Majalisar sun kuma baiwa hukumar hadin kai yadda ya kamata.
Da yake magana da manema labarai Walin Kano, Alhaji Mahe Bashir Wali, ya ce kudin da Majalisar masarautar Kano ke kadashi lokacin Mai martaba Ado Bayero, Naira Biliyan biyu da miliyan dari takwas.
Sai kuma Wali ya ce gabanin rasuwar Ado Bayero, an fitar da wasu kudade da yawansu ya kai Naira miliyan ‘dari tara da tamanin da ‘daya wanda aka biya ‘yan kwamitin gini gidajen Ado Bayero Royal City da ke Darmanawa.
Hakan yasa Mai Martaba Sarkin Kano Mohammadu Sunusi na biyu ya gaji Naira Biliyan ‘daya da Naira dubu ‘dari takwas da casa’in da uku.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum