Yanzu haka dai ana iya cewa bakin ciki ya rikide ya koma hushi, yayin da har yanzu ‘yankwana-kwana a Landan ke ci gaba da kokarin ganin sun kashe wutar gobaran nan da ba a taba ganin irin ta ba nan kusa-kusa.
Wannan yasa yiyuwar shugabanni shan tambayoyi akan karya dokar kare al’umma.
‘Yan sanda sunce akalla mutane 12 ne aka tabbatar sun mutu, yayin da gobarar tayi ta bazuwa a benen mai hawa 24 dake kudancin Landan da yammacin jiya talata, inda ta rutsa da mutane da dama.
Ana sa ran adadin wadanda suka mutun ya karu, yayin da masu aikin kashe gobarar suke bi hawa-hawa domin tabbartar da kashe wutar kurmus da kuma gano wadanda basu iya fita ba.
Facebook Forum