Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar APC Ta Dare Biyu A Jihar Sokoto


APC logo
APC logo

Jam'iyyar APC ta shiga wani takunsaka a jihar Sokoto inda bangarorin Bafarawa da Wamako suka yi hannun riga

Jam'iyyar APC ta rabu biyu a jihar Sokoto inda kowane bangare ya bude nashi ofishin.

Bangaren tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa ya kirawo taron manema labarai lokacin da ya bude nashi ofishin. A wurin bikin bude ofishin suka gabatar da sunayen mutane biyar a matsayin shugabannin riko na bangarensu.Alhaji Abubakar Sadiq Sanyinna shi ne zai shugabanci bangaren.

A wani hannun kuma matamakin ma'ajin jam'yyar na kasa Usman Dan Madami ya sha yin sanarwa a kafofin labarai game da nadin shugabannin riko na jam'iyyar bangaren da gwamnan jihar Aliyu Wamako yake ciki. Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar shi ne Barrister Inuwa Abdulkadir.

To amma bangaren Bafarawa na ganin sanrwar Usaman Dan Madami da nadin shugabannin riko a karkashin Barrister Inuwa Abdulkadir a zaman jabu. Bagaren na ganin cigaba ne na kokarin gwamna Wamako na son kwace jam'yyar. Na hannun daman Alhaji Bafarawa kuma tsohon shugaban ANPP Alhaji Ibrahim Milgoma ya ce duk 'yan bangaren Wamako 'yan PDP ne. Ya ce ba gaskiya ba ne a ce an kaddamar da wani kwamitin riko daban da nasu. Ya ce tun farko shugabannin jam'iyyar na kasa suka bukaci a basu sunayen wadanda zasu rike jam'iyyar kuma sun bayar.

To sai dai an ce akwai wata takarda wadda sakataren kasa na jam'iyyar APC ya sa ma hannu dauke da sunayen 'yan kwamitin riko na jihar. Amma Alhaji Ibrahim Milgoma ya ce wannan takadar ba gaskiya ba ce. Ya ce bangaren Wamako ne ya rubuta wasikar ya kai. Ya ce har yanzu su ne da shugabanni.

Shi kuma Barrister Inuwa Abdulkadir ya ce su ne shugabannin halal da iyayen jam'iyyar suka san da su. Ya ce jam'iyyarsu ce ta tsara cewa duk jihar da gwamna ya shiga APC to shi ne jagorar tafiyar. Domin haka bai kamata wani ya sabawa umurnin iyayen jam'iyyar na kasa ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG