Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jana'izar Karshe Ta Tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro


Jerin gwanon motocin da suka dauko tokar gawar tsohon shugaban Cuba Fidel Castro

Da Safiyar yau Lahadi aka fara shirye shiryen jana’izar karshe ga tsohon shugaban Cuba, Fidel Castro, wanda ya rasu a makon da ya gabata yana mai shekaru 90.

An rufe tokar gawarsa ne a makabartar Ifigenia dake Santiago de Cuba, inda aka yi jana'izar cikin sirri tare da hana ‘yan jarida shiga makabartar.

A wani bikin jana’izar da aka yi a ranar Asabar, shugaba mai ci, Raul Castro, ya gayawa dubun dubatar ‘yan kasar da suka taru a Santiago de Cuba cewa, gwamnati za ta aiwatar da wasiyyar da Castro ya bari, inda ya nemi da kada a gina mutum-mutuminsa ko kuma a saka wa wani gini sunansa.

“Irin koyi da Castro ya ke so mu yi da shi ke nan” In ji shugaba Raul mai shekaru 85, wanda kuma ya yi jawabinsa sanye da kakin soji.

Ya kuma ce Cuba za ta shawo kan duk wani kalubale da hargitsi da barazana da ta ke fuskanta a kokarinta na karfafa tsarin mulkin gurguzu.

A ranar Asabar tokar gawar Fidel Castro ta isa Santiago de Cuba, birnin da ya fara fafutkar juyin-juya-hali.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG