Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Buhari ya Bayyana Aniyarsa ta Sake Tsayawa Takara


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A yau ne dai Janar Buhari ya bayyan aniyyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya a zabe daza ayi mai zuwa, taron dai ya samu halarcin mutane dayawa a babban dandalin taro na (eagle square) a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Tun safiyar yau dai mutane suka rika dafifi a wurin kafin shi Janar Buhari yazo da tashi tawagar, ambaiwa duk manyan baki dama domin fadin albarkin bakinsu, yawancin mutane dai nata fadin albarkacin bakinsu akan Buhari wadansu kuma na fadin irin halin da kasar Najeriya ta shiga, mutane dayawa dai sun bayyana cewa babu wanda zai iya kwato Najeriya kan halin ‘ka’ka nakayi da take ciki sai Janar Buhari.

Idan akazo dandali irin wanan ba’a rabashi da hayaniyar jama’a da kuma masu baiyana ra’ayoyinsu, akwai gwamnoni da yawa da ‘yan majalisar dattawa dakuma ‘yan majalisar wakilai, akwai kuma mutane dasuka fita daga Jam’iyyar PDP suka shigo Jam’iyyar APC duk sun halarta wannan taro a yau, wanan taro ne na kasa baki daya na Jam’iyyar APC ya wakana a eagle square dake Abuja.

Cikin jawaban da Janaral yayi ya baiyana halayen da jama’a suka shiga a tun lokacin da aka fara mulkin demokaradiyya shekaru goma sha biyar da suka wuce, ya kuma nuna rashin gamsuwarsa da yarda ake tafiyar da harkar kasar daga abinda yakama da tattalin arziki, harkar tsaro, da harkar ilmi da suka damu jama’ar kasa baki daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG