Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Trump A Babban Taron Kolin Majalisar Dinkin Duniya


Shugaban Kasar Aurka Donald Trump
Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya gudanar da jawabi a babban taron kolin shugabannin kasashe na Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 a jihar New York.

A jawabinsa shugaba Trump ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, kamar raguwar marasa aikin yi da samar da samar da ayyukan yi da sana’o’i. Ya ce cikin shekaru uku an samarwa da Amurkawa miliyan shida da ayyukan yi.

Trump , ya kara da cewa kazalika Amurka ta shiga jerin kasashen da ke samar da Man Fetur a Duniya, inda wannan ya nuna nasara ce da aka samu a karkashin gwamnatinsa. Sannan ya yi magana akan kasuwanci, inda ya ce shekara da shekaru ke nan, kusan shekaru 10 Amurka tana iyakacin bakin kokarin ta, don inganta huldar kasuwancinta da sauran kasashe, musamman makwabtanta da suka hada da Mexico da kuma Canada. Ya ce suna ci gaba da tattaunawa akan irin wadannan abubuwa.

Shugaba Trump, ya kara da cewa Amurka za ta hadin gwiwa da kasar Birtaniya, a lokacin da take kokarin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai. Ya nuna cewa akwai wasu aiyuka, ko hulda na kasuwanci da za suyi da Birtaniyar.

Batun huldar kasuwanci da Trump ya yi akan huldar Amurka da kasar China, ya ce tun shekarar 2001 da China ta shiga cikin kungiya ko cibiyar kasuwancin Duniya, ake ganin cewa China za ta samu bunkasar tattalin arziki, da fadada hanyoyin kasuwancinta. Amma bayan kusan shekaru 20, sai abubuwa suka canza maimakon aga bunkasar arziki da fadadawar kasuwancinta, sai China ta zo tana cutar Amurka da sauran kasashen Duniya.

Shugaban Trump bai ambaci wani abu na musamman tsakanin Amurka da Najeriya ba, ko wasu kasashen Afirka. Sai dai ya ce akwai tanadi da ake yi domin bunkasa kasuwanci tsakanin Amurka da wasu kasashe da dama a Duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG