Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerard Pique Ya Sanar Da Yin Ritaya Daga Kwallan Kafa


Dan wasan Barcelona Gerard Pique
Dan wasan Barcelona Gerard Pique

Dan wasan bayan Sipaniya da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Gerard Pique ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafar kwararru.

Pique, wanda ya lashe lambobin yabo da yawa karkashin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, da kuma gasar cin kofin duniya ta 2010 tare da tawagar kasar, bai samu tagomashi a kakar wasa ta bana karkashin kocin Barcelona Xabi Hernandez ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa wasan La Liga da za su yi da Almeria ranar Asabar ne zai kasance wasan shi na karshe.

Dan wasan mai shekaru 35, ya kasance dan wasa ne da ke tawagar Barcelona masu buga wasa akai-akai bayan da ya koma daga Manchester United a shekarar 2008, amma a cikin ‘yan shekarun nan ya fara fama da rauni akai-akai. Duk da haka, Edgar Saiz na Eurosport na Spain ya ce sanarwar abin mamakin ce.

Abin mamakin ne sosai domin babu wanda ya yi tsammanin hakan,” in ji shi. “Gaskiya ne saboda rawar da ya taka, ana tsammanin zai yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana, amma yanzu abin ya zama da ban mamaki.”

Shigar ‘yan wasa irin Eric Garcia da Ronald Araujo ya tilasta masa yin kasa a jerin ‘yan wasa a sansanin horos da ‘yan wasa na Nou.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG