Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jigawa Golden Stars Ta Shammaci Su Ahmed Musa

Kyfatin din Najeriya kuma dan wasan Kano Pillars Ahmed Musa (Instagram/ Kano Pillars).
Kyfatin din Najeriya kuma dan wasan Kano Pillars Ahmed Musa (Instagram/ Kano Pillars).

Yanzu Pillars na matsayi na uku da maki 49 yayin da Akwa United ta dare sama da maki 53 a teburin gasar ta Premier a Najeriya.

Burin da kungiyar Kano Pillars ta sa a gaba na daukan hanyar lashe kofin gasar Premier ta Najeriya ya fuskanci matsala, bayan da “Sai Masu Gida” suka sha kaye.

A karshen mako Jigawa Golden Stars ta lallasa Pillars da ci 1-0 a filin wasa na Hadejia.

Yaran na Badaru sun samu lagon Pillars ne a minti na 80 ta hannun dan wasanta Ali Akalla.

Wasan ya kasance ci gaban karawar dadaddiyar hamayya da bangarorin biyu suka sha bugawa.

Kungiyar ta su Ahmed Musa ta yi bakin kokarinta, don ganin ta farke kwallon da aka zira mata a raga amma abin ya ci tura.

Yanzu Pillars na matsayi na uku da maki 49 yayin da Akwa United ta dare sama da maki 53 a teburin gasar ta Premier a Najeriya.

Nasarawa United na matsayi na biyu da maki 49 amma da yawan kwallaye 11 yayin da Pillars ke da kwallaye 7.

Gasar ta Premier ta kammala mako na 28 kenan.

Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa

Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00

Ahmed Musa ya koma kungiyar Kano Pillars, kamar yadda shugabanta Surajo Shu'aibu Yahaya ya tabbatarwa da wakiliyar VOA Baraka Bashir

Ahmed Musa ya koma kungiyar Kano Pillars, kamar yadda shugabanta Surajo Shu'aibu Yahaya ya tabbatarwa da wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG