Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Adamawa ta Karyata Jita-Jitar Cewa ta Kori 'Yan Kato da Gora' da kuma Maharba


‘Yan sintiri da Mafarauta, rike da bindigogi sun taru kofar fadar Sarki a Maiduguri, 4 ga Satumba 2014.
‘Yan sintiri da Mafarauta, rike da bindigogi sun taru kofar fadar Sarki a Maiduguri, 4 ga Satumba 2014.

Kakakin gwannatin jihar Mr. Peter Elisha yace maimakon haka gwamnatin tana shirin kara tallafawa irin wadannan matsa.

Gwamnatin jihar Adamawa ta karyata rahotannin cewa an janye maharba da kuma yan kato da gora, wato Civilian JTF daga fagen daga inda suke taimakawa sojoji da ke yaki da yan bindiga na kungiyar Boko Haram, batun da yanzu ya tada hankulan jama’a.

Cikin kwanakin nan ne dai yan kato d agora da maharban suka taimakawa wajen fatattakar yan Boko Haram a wasu sassan jihar,da hakan yasa jama’a farin ciki.

To sai dai suma maharban sun bayyana aniyarsu na cigaba da taimakawa, tare da yin kira ga sauran gwamnatocin jihohin arewa da suma su kawo dauki,don yiwa mayakan kofar rago.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

XS
SM
MD
LG