Accessibility links

Jihar Borno ta Soma ba Majinyata Dake Asibiti Abinci


Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima,

A wani yunkurin taimakawa talakawa gwamnatin jihar Borno ta fito da shirin ciyarda majinyata dake asibiti kyauta

Gwamnatin jihar Borno ta bullo da wani sabon shirin na samarda abinci kyauta ga majinyata dake kwance a wasu asibitocin jihar domin rage masu irin wahalun da jama'a ke fuskanta.

Gwamnatin ta ce ta san irin matsanancin hali da jama'ar jihar suka shiga sakamakon irin rigingimun da aka dinga fama dasu a jihar domin haka ne ta bullo da sabon shirin. Shirin ya tanadi rabawa majinyata abinci kyauta musamman wadanda ke kwance a asibitocin gwamnati domin saukakawa 'yanuwansu.

Tuni gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai rika lura da ciyar da majinyata da kuma yadda ake dafuwan abincin. Shirin ya soma da wasu manyan asibitoci dake cikin jihar.

Daya daga cikin manyan asibitocin dake Maiduguri babban birnin jihar wato Asibitin Umaru Shehu wakilin Muryar Amurka ya gani da idanunsa abincin da aka dafawa majinyata. Malama Binta Musa jami'ar dake kula da yadda ake dafawa da raba abincin ta yi karin bayani. Tace "kowane safe akwai tsarin da muke bi. Akwai breakfast kamar ti da madara da bonvita. Akwai wani ranan kuma ana basu kunu ne da kosai ko kunu da alale. Wani rana kuma za'a yi panke da ti da madara. Da safe kenan. Da rana kuma akwai ran da za'a basu kaza kamar sau biyu a sati ko Litinin da Alhamis haka. Muna yin su sipageti. Muna yin su jolof rice. Muna yin rice and stew..." Wato kowace rana tana da nata tsarin.

Dangane da ko wasu masujinya suna bukatar abinci na musamman ko zasu iya basu sai Malama Binta Musa tace "kamar masu diabetes (wato masu ciwon sikari) ana iya basu abun da ba na shuga ba kaman kuskus. Wadanda kuma basa cin gishiri za'a yi masu miyansu mara gishiri"

Wakilin Muryar Amurka ya zanta da wasu majinyatan. Malam Shehu Dogara wanda yake kwance yace "ana kawo abinci kowane lokaci kuma muna ci sau uku a rana daya. Da safe muna samun kunu da rana su kawo tuwon laushi ko shinkafa ko taliya" Da aka tambayeshi yadda abincin yake sai yace "Ba banbanci da na gida kuma ko ba'a sake kawowa ba abincin yana ishemu" Shi ma Malam Iliya yace "Abinci, muna samun abinci".

XS
SM
MD
LG