Accessibility links

Duk da ragistan da ta yi a jihar Borno da alamu jam'iyyar APC ta rabu biyu sabili da rashin amincewar wasu 'yan jam'iyyar dangane da rabon mukamai

A jihar Borno jam'iyyar APC ta soma samun rarrabuwan kawunan 'aya'yanta.

Wani bangaren jam'iyyar ya zargi gwamnan jihar Kashim Shettima da nuna son kai wajen raba mukamai. Amma gwamnan ya musanta hakan yana cewa batun ba gaskiya ba ne. Ya ce siyasa ta gaji haka, wato samun rabuwar kawuna. Ya ce zasu warare matsalar cikin ruwan sanyi.

Irin wannan matsalar a cikin jam'iyyar ta soma fitowa fili ne lokacin da sakataren jam'iyyar na kasa ya kaddamar da sabbin shugabannin jam'iyyar na jihar Borno a makon jiya a garin Maiduguri a karkashin jagorancin gwamnan jihar Kashim Shettima. Amma wasu a wani bangaren jam'iyyar sun ce basu amince da nadin ba sabili da haka suka kirawo taron manema labarai inda suka bayyana rashin amincewarsu. Sun zargi gwamnan da nuna son kai wurin zabo sabbin shugabannin.

Alhaji Ibrahim El-Zubair wanda ya jagoranci bangaren da bai amince da nadin sabbin shugabannin ba ya ce abun da aka yi haramtacce ne domin akwai ka'idojin da kwamitin jam'iyyar na kasa ya shimfida. Ya ce ba'a bi tsarin jam'iyyar ba. Ya ce wasu 'yan tsiraru suka zauna suka rubuta sunayen mutane. Ya ce sakatren jam'iyyar na kasa bashi da hurumin zuwa ya kaddamar da shugabannin jiha domin ba aikinsa ba ne.Ya ce zasu nemi hakinsu kuma dole a yi gyara.

Kodayake basa tunanin ficewa daga jam'iyyar amma ya ce gwamnan jihar bai nuna masu halin uba ba. Shi gwamnan zuwa jam'iyyar ya yi. Idan yana son ya bar jam'iyyar ya bari amma su suna nan daram.

To sai dai gwamnan jihar Bornon ya ce siysa ta gaji haka amma matsalar ta cikin gida ce. Ya yi imani cewa zasu warware matsalolinsu komi tsanani.Shi ko Sanata Kaka Malam Yale shugaban rikon jam'iyyar ya ce batun ba haka yake ba. Ya ce sauran jam'iyyun dake cikin APC a jihar sun fi ANPP samun mukamai a kwamitin jihar. Mataimakin shugaba da shugaban matasa duk daga CPC suka fito.

XS
SM
MD
LG