Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Biyu Daga Cikin Wadandan Su Ka Sace Ba’amurke Sun Fada Raga


Wasu masu garkuwa da mutane
Wasu masu garkuwa da mutane

Dubun biyu daga cikin mutanen da su ka sace wani Ba'amurke a Nijar su ka ketaro da shi Najeriya kwanan bayan ta cika. Hakan ya biyo bayan yinkurinsu na shirin daukar fansar kashe shida daga cikinsu da aka yi tun farko.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama biyu daga cikin mutanen nan masu garkuwa da mutane na kasa da kasa, wadanda su ka sace Ba’amurken nan, Philip Walton a gonarsa da ke kauyen Masallata a kasar Nijar su ka ketaro da shi Najeriya.

Wata sanarwar da Kakakin ‘Yansandan Najeriya, Frank Mba ya raba ma manema labarai, ta ce wadanda aka kama din su ne Aliyu Abdullahi, dan shekaru 21, wanda ake wa lakabi da Mallam; sai kuma Aliyu Umaru, mai shekaru 23, wanda ake wa lakabi da Kwattikusu kuma dukkansu ‘yan jahar Sakkwato ne.Mutum biyun da aka kama na da daga cikin gungun ‘yan Najeriya da Nijar 15 masu sace mutane wadanda wani mai suna Bate Dan Alhaji da Dan Buda su ke jagorantarsu.

An kama wadannan mutanen biyu ne sanadiyyar wani bayani na sirri da ke nuna cewa suna wani sabon shirin kuma na garkuwa da mutane, a matsayin ramuwar gayyar kashe shida - hudu ‘yan Najeriya, biyu ‘yan Nijar – da sojojin kundunbalar Amurka su ka yi yayi aikin kubutar da Ba’amurken.

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya ce zai cigaba da musayar bayanan sirri da takwarorinsa na kasashen Afurka Ta Yamma da kuma daukar matakan karfafa tsaro a kan iyakokin don maganin miyagu masu aika aika a kan iyakokin yankin.

Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:20 0:00

Karin bayani akan: Najeriya, sojoji, da kasar Nijar.

XS
SM
MD
LG