Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yaki sun Tarwatsa Rumbun Hatsi da Wasu Wuraren 'Yan Daular Islama


Omar al-Shishani da Kungiyar Daular Islama.
Omar al-Shishani da Kungiyar Daular Islama.

Wata kungiyar sa ido ta ce wasu hare-haren jiragen yakin da Amurka ta jagoranci kai wa.

Wata kungiyar sa ido ta ce wasu hare-haren jiragen yakin da Amurka ta jagoranci kai wa, sun dibgi wasu wuraren 'yan Kungiyar Daular Islama akalla a larduna biyu na Syria a tsawon daren jiya.

Kungiyar sa ido kan al'amuran 'yancin dan adam a Syria mai hedikwata a Burtaniya, ta fadi yau Litini cewa, hare-haren sun tarwatsa wani babban rumbun hatsi da wasu wuraren mayakan a Aleppo da Raqa.

Kungiyar sa idon ta ce farar hula ke gudanar da wannan babban rumbun hatsin, kuma ga dukkan alamu, akwai wadanda aka rutsa da su. Ba a dai tabbatar da wannan rahoton ba.

An ce sauran hare-haren kuma sun shafi mashigar babbar tashar iskar gas ta kasar, a wani al'amari mai kama da gargadi ga 'yan kungiyar ta Daular Islama na su fice daga wurin.

Tun ranar Talatar da ta gabata jiragen yakin Amurka, tare da goyon bayan na kasashen Larabawa kawayenta, su ka fara kai jerin hare-haren jiragen sama a Syria. An fara kai hare-haren jiragen sama a makwabciyar kasa ta Iraki kuma tun daga watan jiya. Hare-haren jiragen saman da aka kai a Irakin sun taimaki dakarun Iraki da na Kurdawa wajen yin wasu nasarori kan mayakan sa kan.

Mayakan Daular ta Islama sun kwace yankuna masu fadin gaske a kasashen biyu a wannan shekarar.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce da Amurka ba ta zaci kungiyar Daular ta Islama da wasu 'yan bindigar da ke Syria sun kai haka ba, kuma ta zaci sojojin Iraki na da karfin yakarsu.

Mr. Obama ya fadi a shirin Gidan Talabijin din ABC mai suna '60 Minutes,' a jiya Lahadi cewa, ba daidai ba ne cewar da wasu a birnin Washington ke yi cewa, da ace Amurka ta samar da kayan yaki ga 'yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi tun shekaru biyu da su ka gabata da Syria ta sami barata a yanzu.

XS
SM
MD
LG