Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin 'Yan Sandan Venezuela Da Aka Sace Ya Yi Luguden Wuta


Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya ce wani jirgi mai saukar ungulu mallakar rundunar 'yan sanda, wanda aka sace, ya yi barin wuta kan ginin Ma'aikatar Cikin Gida da kuma Kotun Kolin kasar a jiya Talata, al'amarin da ya kira 'harin ta'addanci,' wanda masu niyyar hambarar da shi su ka kai.

Shugaba Maduro, ya sha alwashin kama wadanda su ka kai harin, wanda ba a samu rahoton rauni sanadinsa ba.

Ministan Sadarwa da yada labarai Ernesto Villegas, daga baya ya ce jirgin ya yi harbi har sau 15 a kan ginin ma'aikatar sannan ya jeho gurnet-gurnet akalla hudu kan ginin Kotun Kolin.

Villegas ya ce wani Osacar Perez ne ya tuka jirgin. Wani faifan bidiyon da aka yada ta kafar sada zumunci na nuna Perez tsaye gaban wasu mayaka dauke da bindigogi, ya na mai kiran da a yi tawaye ma gwamnatin Maduro ta, abin da ya kira, 'kama-karya,' ya na mai kira ga Shugaba Maduro da ya sauka, sannan kuma kasar ta Venezuela ta gudanar da sabon zabe.

Wasu masu adawa da Maduro sun yi ta zargi a kafafen sada zumunci, cewa gwamnati ce ta tsara harin na jiya Talata don ta samu hujjar fatattakar 'yan adawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG