Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada a Dorawa Kowa Laifin Sace Daliban Chibok-inji Gwamnan Sokoto


Gwamnan Sokoto Aliu Magatakarda Wamako

Yayin da yake karbar malaman da suka yi zanga-zangar lumana domin nuna takaicinsu akan sace daliban Chibok gwamnan Sokoto Aliyu Magatakardan Wamako yace yanzu ba lokaci ba ne na dorawa kowa laifi.

Duk da jam'iyyarsa ta APC tayi kakkausar suka akan abun da ta kira tafiyar hawainiya da tace gwamnatin tarayya na yi wurin ceto daliban da aka sace a garin Chibok jihar Borno, gwamnan jihar Sokoto Aliyu Wamako yace yanzu ba lokacin dorawa kowa laifi ba ne.

Gwamnan yayi jawabinsa ne ga 'yan kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Sokoto da suka gudanar da zanga -zangar lumana ta nuna alhini da bacin rai akan kasa gano daliban har tsawon makonni biyar. Masu zanga-zangar sun yi maci ne zuwa fadar gwamnan.

A jawabinsa yace na farko kowa yayi addu'a Allah Ya kawo daliban lami lafiya ga iyayensu. Yace kada Allah Ya sa a cutar da su yayin da suke hannun 'yan Boko Haram din. Yace abun ya riga ya faru. Haka Allah Ya kaddara zai faru ta hannun miyagun mutane da suke kiran kansu Boko Haram. Yayi addu'ar Allah Ya tonasu Ya kuma karyasu ya kuma kare na gaba. Yace halin da ake ciki ba hali ba ne na raba laifi, wato a ce ga mai laifi ga mara laifi. Kamata yayi a hada kai a ceto yaran. Yace duk wata magana da ba haka ba bata da wani anfani.

Shugaban kungiyar malaman reshen Sokoto Cika Maidamma Alkamawa yace bayan daliban da aka sace suna kuma jajantawa akan malamai fiye da 170 da aka kashe a rikicin na Boko Haram tsakanin jihohin Borno da Yobe. Abun da ya dada bata masu rai shi ne yadda gwamnati tayi biris da abubuwan da suka faru.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG