Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafa Kotun Cin Hanci Ba Sabon Abu Bane – inji Lauyoyi


EFCC
EFCC

Batun kafa kotuna na musamman domin yin shari’a akan wadanda ake tuhuma da satar kudaden gwamnati ya tayar da kura, inda wasu suke gani hakan shine ya dace, wasu kuma suna fargaba kar kotunan su zama wajen tuhumar wasu da kyale wasu.

Mallam Ibrahim Bello Jahun, malami ne a tsangayar koyon aikin shari’a a Jami’ar Amadu Bello dake Zariya yayi karin haske game da ayyukan wadannan kotuna.

“Ace an yi sabuwar kotu na musamman, domin bin bahasin shari’a na mutanen da ake tuhumar su da cin hanci da rashawa, wani abu wanda dama ba sabo bane.”

Masu fashin baki na gani sabuwar gwamnatin APC zata fi haske fititar ta ne a yaki da cin hanci da rashawa ga jami’an tsohuwar gwamnatin PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki. Ambasada Ibrahim Kazaure, kusa ne a Jam’iyyar PDP.

“Idan binciken ba wadansu kadai za’a yiwa ba, domin duk wanda ya dibi kudin Najeriya ya dawo da su, ai wannan babu laifi” a cewar Mr. Kazaure.

Ana danganta matsalar cin hanci da rashawa a da zama musabbabin hana jama’a cin moriyar demokradiyya a nahiyar Afirka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG