Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamar Somaliya Dubu 750 Suke Fuskantar Mutuwa Sabo Da 'Yunwa Nan Da Nan

Wata mace daga kudancin Somaliya take rike da danta mai fama da 'yunwar abinci mai gina jiki.

Majalisar Dinkin Duniya tace fiye da rabin al’umar Somaliya milyan hudu suna cikin fitina ganin bala’in yunwa daake kara bazuwa cikin kasar, har kamar mutane dubu 750,000 suna cikin hatsarin fuskantar mutuwa.

Jiya litinin ce Majalisar saki wani rahoto da ya ce fitinar ta kai sassa shida na kasar, kuma ana ji zai kara bazuwa cikin wata hudu masu zuwa har sai fa idan an kara agaji da ake bayarwa.

Sashen nazarin harkokin abinci mai gina jiki a Somalia na majalisar, yace yawan mutane da suke mutuwa sakamkon ‘yunwa a kudancin kasar ya dara abinda aka saba gani a musiba irin wannan. Rahoton yace galibin gidaje suna fuskantar karancin abinci sosai sakamkon fari da kuma rashin kudi.

Hukumar kasa da kasan tace dubun dubatar mutane ne tuni suka mutu a Somalia, galibinsu yara.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG