Accessibility links

Yan gudun hijirar Ivory Coast sun koma kasarsu

  • Jummai Ali

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace yan kasar Ivory Coast dubu saba’in wadanda suka arce daga kasarsu a saboda tarzomar bayan zabe sun koma kasar su.

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace yan kasar Ivory Coast dubu saba’in wadanda suka arce daga kasarsu a saboda tarzomar bayan zabe sun koma kasar su.

Hukumar tace a yan watanin da suka shige ne yan gudun hijira suka koma yammacin Ivory Coast domin radin kansu. Ana kyautata zaton fiye da yan Ivory Coast dubu dari da saba’in da uku ne suka tsalaka zuwa Liberia bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan nuwamban a kasar da aka yi rikici akan sakamakonsa da kuma tarzomar data biyo baya. Wasu yan Ivory Coast dubu ashirin da shidda kuma sun gudu zuwa wasu kasashe a yankin.

Hukumar lura da yan gudun hijira tace a ranar alhamis ta bude, ko kuma ta kafa sansanin yan gudun hijira na shidda a Liberia domin yan gudun hijira Ivory Coast dubu ashirin da bakwai wadanda da suke zaune a wasu wuraren a gabashin Liberia su samu matsuguni. Hukumar tace wannan sansani shine zai zama na karshe da hukumar zata bude a Liberia a yayinda matakan tsaro ke ci gaba da ingantuwa a Ivory Coast.

Akalla mutane dubu uku ne aka kashe a tarzomar bayan zaben Ivory Coast. Idan kuma ba’a mance ba a watan Afrilu sojojin dake biyaya ga shugaba Alassane Ouatara suka kama tsohon shugaba Laurent Gbagbo.

XS
SM
MD
LG