Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: An Kashe Mutane Biyar A Wani Harin Bindiga Da Aka Kai Kan Ma'aikatan Gona


Gona a Kamaru
Gona a Kamaru

Akalla ma’aikatan noman ayaba biyar ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a ranar Juma’a a yankin Kudu maso yammacin Kamaru da ke fama da rikicin ‘yan aware, in ji wani shugaban kungiya.

Maharan da ba a san ko su wanene ba sun harbe wata babbar motar daukar ma’aikata ta Kamfanin Raya Kasar Kamaru wato Cameroon Development Corporation (CDC) a turance– babban kamfanin sarrafa noma na kasar wanda a baya ‘yan awaren Anglophone dauke da makamai da ke fafutukar neman ‘yancin kai suka yi wa ma’aikatansu hari.

An kai harin ne da misalin karfe 5:30 na yamma, a daidai lokacin da suke kusa da garin Tiko bayan ma'aikatan sun kammala aikinsu, in ji Gabriel Mbene Vefonge, shugaban kungiyar kwadagon noma da hadin gwiwar ma'aikatan Kamaru (CAAWOTU).

"Sun fara harbin direban don su dakatar da motar, inda suka kashe wasu ma'aikata uku da suke zaune a gaba," Vefonge ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho, inda ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyar baki daya.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. CDC, 'yan sanda, da wakilin 'yan aware ba su amsa bukatar jin ta bakin su ba.

Wadanda suka tsira da rayukansu a harin ana yi musu jinyar raunukan harbin bindiga a asibitin CDC Cottage Tiko, wata ma’aikaciyar jinya da ke wurin, ta kuma ki bayar da karin bayani.

Rikicin 'yan awaren, wanda ya samo asali tun tsawon shekarun da suka gabata, sun dade suna kokawa kan wariya daga gwamnatin Kamaru masu harshen faransa, lamarin da ya yi sanadiyar zubar da jini a cikin 2017 bayan da aka murkushe wasu masu zanga-zangar.

Tun daga wannan lokacin, an kashe dubban mutane a yankin tsakiyar Afirka, kuma 'yan tawaye da sojojin gwamnati sun yi ta tafka munanan ta'asa.

A watan da ya gabata ne dai gwamnatin kasar ta ce ba ta ba wa wata kasa damar gudanar da tattaunawa da 'yan awaren don taimakawa wajen kawo karshen rikicin ba, duk kuwa da cewa kasar Canada ta amshi bukatar yin aiki da tsarin zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG