Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Na Mayar Da 'Yan Gudun HIjirar Najeriya Karfi Da Yaji


Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mai da ‘yan gudun hijirar Najeriya da kasar Kamaru ke yi karfi da yaji zuwa jihar Borno mai fama da tashin hankali, ta na mai bayyana hakan da saba wa dokar kasa da kasa.

Hukumar ta ce hankalinta ya tashi saboda al’amarin da ya yi kama da wani salo na tilasta ma mutune komawa. Zuwa yanzu a wannan shekarar Hukumar ta ba da rahoton cewa kasar Kamaru ta tasa keyar ‘yan gudun hijirar Najeriya 385 karfi da yaji zuwa jahar Borno, akasarinsu a wannan watan.

A baya-bayan nan, Hukumar ta ba da rahoton cewa ran 17 ga watan nan na Afirilu an tilasta ma ‘yan Najeriya 118 masu neman mafama komawa Najeriya.

Kuma mako guda kafin nan, wato ran 10 ga watan Afirilu, kasar ta kori ‘yan Najeriya 160 masu neman mafaka.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG