Daga bisani kuma sai aka samu wasu wuraren a jihohin Imo da Enugu, a farkon wannan shekarar kuma sai gashi an sami kamfanin a jihar Ondo.
Yanzu haka kamfani ya bullo a jihar Ogun, shi dai kamfanin na jarirai, wasu mutane ne masamman mata ke tattara mata masu ciki a waje daya, suna kula dasu, sannan da zaran sun haihu sai su karbe jaririn su saida ga mabukata.
A binciken da muka gudanar ya nuna cewa wasu jariran ana sayansu ne domin yin sidabaru, wasu kuma wadanda basu taba haihuwa bane ke sayensu su maida su a matsayin 'yan yansu.