Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Trump Da Babban Jami'i Mai Kula Da Kudinsa Na Fuskantar Tuhuma


Trump

An sami kamfanin Donald Trump da kuma babban jami’i mai kula da harkokin kudinsa da laifukan da suka samo asali daga masu bincike na New York kan harkokin kasuwancin tsohon shugaban kasar.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin wasu mutane biyu da suke da masaniya kan lamarin wadanda suka yi magana da kamfanin dillanci labarai na Associated Press bisa sharadin sakaya sunansu.

Sai dai an ci gaba da sirranta zargin tuhumar kan Trump Organization da babban jami’in mai kula da harkokin kudi, Allen Weisselberg a ranar Laraba.

Trump ya ce kamfaninsa bai aikata wani laifi ba kuma ya yi shakulatin bangaro ga binciken a matsayin bita-da-kullin siyasa.

Binciken ya hada da abin da kamfanin ya bawa shugabanninsa, ciki har da amfani da gidaje da motoci da biyan kudin makaranta.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG