Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yi Watsi Da Dage Dakatar Da Twitter


Twitter
Twitter

A lokacin da mataimakin kakakin majalisar Idris Wase ya bukaci a yi kuri’a kan shawarar dage dakatarwar da aka yi wa Twitter, mafi akasarin ‘yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da shawarar.

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da dage dakatarwar da aka yi wa Twitter a kasar.

Matakin majalisar ya bayyana ne sa’adda take nazarin rahoton kwamitin ta na hadin gwiwa da ya yi bincike kan turka-turkar da ta haddasa gwamnatin tarayya dakatar da shafin yanar gizo na Twitter a kasar.

Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Gwamnatin Najeriyar ta dakatar da ayukan shafin na Twitter a fadin kasar, bayan da ta zarge shi da hura wutar rikice-rikice a sassa daban-daban na kasar.

‘Yan Najeriya da dama, ciki har da wasu masu fada a ji, kai har ma da kasashen Turai sun yi Allah wadai da matakin na gwamnatin Najeriya.

Wannan ne ya sa majalisar wakilai ta soma nazarin matsalar, tare da dorawa kwamitocinta na sha’anin watsa labarai, da na fasahar sadarwa ta zamani, da na tsaro da kuma na shari’a, alhakin bincike kan lamarin.

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamaila (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamaila (Facebook/House of Reps, Nigeria)

To sai dai daya daga cikin shawarwarin kwamitin na hadin gwiwa ya janyo cece-kuce, wanda ke neman gwamnati ta yi la’akari da mummunan tasirin da dakatar da ayukan Twitter zai yi ga ‘yan Najeriya da ke neman abinci ta hanyar shafin, ta kuma dage dakatarwar da tayi masa.

Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar Toby Okechukwu ne ya nemi bukatar yin gyara a kan wannan shawarar da ke cikin rahoton kwamitin.

A lokacin da mataimakin kakakin majalisar Idris Wase ya bukaci a yi kuri’a kan shawarar, mafi akasarin ‘yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da shawarar.

Rahotanni na baya-bayan nan dai sun nuna cewa an soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin na Twitter, duk da yake kamfanin ya ki amincewa da wasu bukatun gwamnati, da suka hada da rufe shafin jagoran ‘yan awaren IPOB mai fafutukar kafa kasar Biayafara.

XS
SM
MD
LG