Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanawa Na Fatan Gwamnatin Buhari Za Ta Yi Dasu Wannan Karon


Nigeria Election
Nigeria Election

Kwana daya kenan bayan da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi takardar shaidar cin zabe a karo na biyu daga hannun shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu.

Wannan shine karo na biyar da shugaba Buhari ke samun gagarumin rinjaye a jihar Kano tun bayan da ya fara takarar shugabancin Najeriya a shekara ta 2003.

Sai dai duk da haka da dama mutanen Kano sun koka wajen samun ababubuwan da zasu habbaka harkokin tattalin arziki ta bangaren noma da ci gaban masana’antu, da kasuwanci da jihar ta shahara akan su.

Wasu matasa sun bayyana mamakin su akan yadda shugaban ya mayar da Kano saniyar ware a cikin shekaru 4 na gwamnatin sa.

Suma dai dattawan jihar sun tabbatar da yanayin rashin raba kayayyakin habbaka rayuwar Jama’a daga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari cikin shekaru 4 baya, musamman idan aka kwatanta da rawar da take takawa wajen nasarar shugaban a fagen zabe.

A yayin walimar cin zabe da magoya baya suka yi, shugaban kwamitin yakin neman zabe na shugaba Buhari a jihar Kano. Alhaji Sabo Nanono yayi Karin haske game da lafazin da yayi cewa, yanzu kanawa suke bin shugaba Buhari bashi.

Shi kuwa Janar Bashir Salhi Magashi cewa yayi, sun daura damarar ganin Kano ta rabauta da ayyukan gwamnatin Buhari a wannan Karo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG