Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: An Shiga Rana Ta Biyu A Shari'ar Dan China Da Ake Zargi Da Kashe Budurwarsa


Mr Frank Geng Quatrong a kotu.
Mr Frank Geng Quatrong a kotu.

Yau Alhamis aka shiga rana ta biyu da fara sauraron shiri’ar mutumin kasar China nan Mr Frank Geng Quatrong wanda ake tuhuma da kisan gilla ga Ummukulsum Sani Buhari a Kano a ranar 16 ga watan satumba.

Jiya mahaifiya da kuma kanwar Ummukulsum wato Fatima Zubair da Asiya Sani Buhari su ka gabatar da shaida kan yadda Mr Frank ya shiga har cikin gidan su ya caccakawa Ummukulsum wuka a kirjinta, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarta.

Da yake gabatar da shaida a gaban babbar kotun Kano dake Miller Road, karkashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, daya daga cikin makwaftan marigayiya Ummukulsum Mustafa Abubakar ya fadawa kotun cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Satumba da misalin karfe tara na dare, ya ji ana dukan kyauran kofar gidan su Marigayiya, kuma lekowar sa ke da wuya sai ya hangi Mr Frank Geng, wanda dama ya saba zuwa, yace dashi "ya kamata ka saurara da buga kofar haka, tunda sun ji zasu bude."

Malam Mustafa ya ci gaba da fadawa kotu cewa, “daga bisani ne, sai naji hayaniya ta kaure a cikin gidan, al’amarin da ya ja hankali na na shiga cikin gidan da sauri. Koda shiga ta sai na iske Mr Frank a cikin daki yana caccakawa Marigayiya Ummukulsum wuka a kirjinta, kuma nan take na kama wuyan rigarsa, na janyeshi daga kanta tare da kwace wukar dake hannun sa. Ita kuma Ummukulsum tana kakari jinni na malala daga cikinta. Ganin haka ya sanya Mr Frank Geng ya fice daga dakin ta taga, kuma ya ranta a na kare daga gidan, kafin daga bisani sauran Jama’a su kama shi.”

Daga nan, a cewar Malam Mustafa cikin dimuwa da firgici suka yi kokarin daukar Ummukulsum zuwa asibiti, kuma kafin isa asibitin rai ya yi halin sa.

Shi ma mai bada shaida na 4 a gaban kotun, Jami’in dan sanda da ya jagoranci ayarin Jami’an da hukumar ‘yan sanda ta Kano suka gudanar da bincike bayan afkuwar lamarin, Insifeto Chindo Chiwa, ya fadawa kotun cewa, a ranar 17 ga watan satumba, wato kwana guda bayan Mr wakanar al’amarin, Mr Frank Geng ya shaida musu cewa, tabbas ya caccakawa Ummukulsum wuka a kirjinta kuma hakan ya biyo bayan cizon da ita Marigayiya tayi masa a hannun sa na hagu ne bayan da wata hayaniya ta kaure a tsakanin su.

Insifeto Chindo yace Mr Frank Geng ya sanar da ‘yan sanda cewa, ita marigayiya Ummukulsum Sani Buhari ce ta nemi suyi soyayya da ita ta hanyar wata kawarta a shekara ta 2020. Sai dai bayan soyayyar su tayi nisa, sai Ummukulsum ta auri wani mutum a watan Fabarerun bana. Amma bayan watanni 6 sai auren ya mutu, al’amarin da ya sanya suka dawo da alakar su.

Babban lauyan gwamnati kwamishinan shari’a na jihar Kano Barrister Musa Abdullahi Lawan shine ke jagorantar lauyoyin dake kokarin tabbatar da tuhumar kisan Ummukulsum Sani Buhari akan saurayinta Mr Frank Geng kuma shine ya gabatar da shaidu guda biyu a gaban kotun a zaman na yau. Yayin da Barrister Muhammad Dan’Azumi ke kare wanda ake tuhuma, inda yay i tambayoyi ga wanda suka suka gabatar da shaida.

Tuni dai alkalin kotun mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dade zaman kotun zuwa gobe Juma’a domin ci gaba da sauraron karin shaidu da lauyoyin gwamnati zasu gabatarwa kotu.

XS
SM
MD
LG