Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Manoma Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Koma Bayan Da Noma Ke Samu Saboda Barazanar Tsaro


Gwamnatin Najeriya ta ce shirinta na bunkasa fannonin tattalin arziki marasa alaka da bangaren mai, na haifar da sakamako mai kyau ta fuskar habaka tattalin arzikin kasar.

Sai dai manoman kasar na ci gaba da kokawa kan koma bayan da noma ke samu saboda barazanar tsaro.

Tun kimanin shekaru biyar da suka shude, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti na musamman akan wannan manufa ta raya fannonin samun kudade marasa nasaba da albarkatun mai, da nufin rage dogaro da kasar keyi akan kudaden cinikayyyar man.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan Jigawa Badaru Abubakar aikin kwamitin nasu ya fara haifar da sakamako mai alfanu.

A cewar gwamna Badaru tuni tasirin wannan tsari ya bulla yankunan karkarar Najeriya.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma Najeriyar ke korafi akan jinkirin samun tallafin gwamnati a kasar.

Kamar yadda Arc Kabiru Ibrahim shugaban kungiyar Manoman Najeriya, ya yi karin haske a kai.

Yace baya ga haka, tsaro shine babbar matsalar da ke dakile cigaban manoma da kuma dakushe burin su na wadata kasa da abinci.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dubi ra’ayoyi

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG