Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamin Ilimi Kunkumi ne da Ya Haifar da Boko Haram


Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima

Yayin da yake karbar daliban jihar Borno da suka dawo daga gasar karatun Kur'ani Mai Tsarki, gwamnan jihar yace karamin sani ya fi ciwo zafi kuma shi ne ya haifi kungiyar Boko Haram.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace karamin sanin ilimin addinin Islama ne, ya jefa kasar cikin wannan halin kaka-ni-ka-yi wanda yace ya fi ciwo zafi.

Gwamnan yayi jawabin ne lokacin da yake karbar tawagar daliban da suka dawo daga gasar karatun Kur'ani Mai Tsarki, karo na ashirin da takwas da aka yi a jihar Jigawa. Yace mutanen dake da karamin ilimin addinin Islama ne suka kaucewa hanya suna bayyana abun da ya sabawa addinin. Karamin sanin shi ne ya jefa kasar, musamman yankin arewa maso gabas, cikin halin da suka samu kansu yanzu. Yace da ace sun san Kur'ani ne ba zasu samu kansu cikin wannan kwamachalar ba.

Gwamnan ya cigaba da cewa gurbatacciyar fasarar Kur'ani ce ta jefasu cikin matsalar. Yace ya zama wa shugabanni dole su koma tafarkin koyaswar Annabi Muhammed (S.A.W.) domin ta hanyar ce kawai za'a samu sauki game da abubuwan dake faruwa da ma neman tsira baki daya. Ko a wurin yaki mata da yara da wuraren ibada addinin Islama bai yadda a tabasu ba. Kodama coci ne ana ma karesu ne baki daya. Amma 'yan kungiyar Boko Haram suna yin abun da suke so. Suna kone masallatai da coci da gidajen mutane da suna su musulmai ne. Abun da suke yi ba koyaswar addini ba ne.

Sheikh Tijjani Umara shi ya jagoranci daliban zuwa fadar gwamnatin. Bakwai daga cikinsu sun samu nasara a gasar. Yace 'yan bokon a Borno su ne suke kula da Kur'ani domin haka a wurinsu boko halal ne. Yace idan sun kula da Kur'ani za'a samu zaman lafiya da masalaha.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG