Accessibility links

Mutum na biyu da ya kira kanshi sojan Najeriya, ya fito yayi korafi akan halin da rundunar sojan da yake tare da su ke ciki, dangane da yaki da kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram. Ibrahim Ka'almasih Garba na sashen Hausa ya tattauna da shi.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Me ke tafe da kai?

Soja: To, gaskiya an kawo mu nan, wata daya da wani abu. Ba, abinci ma da ake bamu, ba wani abunnan bane, har ma fada zaka ga sojoji suna fada akan abinci. Kuma ba wani “allowance” da aka bamu. Muna nan, ko kayan fadanma da muke dasu, ba wani abu bane. To, mu dai roko muke dai, ga gwamnati tayi kokari, ta duba abunda muke. Mu kananan, mune ake bawa wahala ba manyan ba.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Ba ance an wadata ku da kayan aiki da kuma abinci saboda ku iya fuskantar Boko Haram ba?

Soja: To wannan dai za’ a iya fada, bamu sani ko suna kan abunnan din bane, amma dai yanzu abinci baya isanmu. Ruwan farko ma da akayi, haka ma kayan mu duka suka jike. Abun idan ka gani, abun tausayi. Uniform dinma ba’a bamu ba. Kayan abunnan wanda zamu sa “tent”, babu.

Ibrahim Ka’almasih Garba: To baku gabatar da koke-kokenku ga manyan sojojin da kuke karkashinsu ba?

Soja: To kasan aikin, yanda yake. Ba yanda zaka ce. Kace ga na gaba da kai, yayi laifi. Haka aikin yake.

Ibrahim Ka’almasih Garba: To dangane da kayan fada, yaya zaka kwatantasu da na Boko Haram?

Soja: Gaskiya abunda zan fada maka, kayan da suke da shi yafi namu. Domin ranar da muka zo, washegari suka yi “attacking” namu, ba yanda zamu yi dasu. Allah dai kawai Ya tsare mu, muka abunnnan, amma mun shiga kawai, muna shiga sun shigo mu, gaba sune baya sune, mun ci sa’a babu “casualities”, kuma da yake mu kasan “we are professionals”.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Kafin a kaiku Maiduguri, an ce an baku horo na musamman, ba haka bane?

Soja: To kasan soja, an riga an horas da mu. Matsalar kayan aiki ne. Wadannan ba wasu mutane bane wadanda za’a ce, in akwai kayan aikin, kwana uku mun riga mun gama da su. Suna cikin daji, duk an riga an kewaye su. Kwana uku ma yayi yawa, zamu gama da su.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Me yasa ba’a wadata ku da kayan aiki da abinci?

Soja: Gwamnati ce bata samarda wannan, ba don da ta samarda, manyan zasu bada, in kuma sune gwamnati ta bayar dole mayan su san abunda zasu yi.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Wace kira kake da ita ga hukumar sojojin Najeriya da kuma gwamnati dangane da wannan yaki da ake yi?

Soja: To, ni dai suyi kokari wannan abin yaya abina, su turo mana kayan aiki bawai a tsaya ana ta “delay” na abubuwan ba tunda damuna na zuwa, wuri na kuma mu bamu ga an shirin mana na kayan damuna kasan ruwan sama.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Kace abinci baya isan ku, to yaya kuke rayuwa?

Soja: To, kasan daji muke akwai magwarori abinda muke abinnan kennan dasu, shine yake dan tallafa mana mangwaro.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Kana nufin sojojin Najeriya dake yaki suna dogara ne ga magwaro a daji da sauran itatuwa?

Soja: To kaima kasan dan adam, kuma soja duk inda yake ko yaya yake akwai abincin isar mu ne baya yi.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Don haka me kuke ci?

Soja: Za’a kawo abincin mutun goma, wa mutun talatin-arba’in. Magwaron ne, shi muke sha tun kafin ya fara nuna muke shan shi, in kuma sunce abinnan ne, su turo “civilian” su shigo dajin su gani, daga su gwamnatin tarayyan da ta turo su, su ganewa idonsu wurin da muke da wahalan da muke sha.

Ibrahim Ka’almasih Garba: Kana da Karin bayani?

Soja: Bani da wani Karin bayani sai dai Allah yasa su ji koke-koken mu su yi mana abunda muke so.


Har yanzu sashen Hausa yana neman hukumomin Najeriya su mayar da martani dangane da kalaman wadannan mutane.
XS
SM
MD
LG