Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Austria Zata Rufe Masallatai Ta Kuma Kori Limamai


Masallacin Yan Turkiya

Gwamnatin Austria mai tsaurin ra’ayi ta fada a yau Juma’a cewa tana shirin rufe masallatai bakwai kana ta kori limamai akalla 40 da iyalansu, a wani matakin kawar siyasar Islama da kuma hana kungiyoyin addini samun kudade daga kasashen waje.

Ministan harkokin cikin gida Herbert Kickl na jami’iyar Freedom Party mai ra’ayin rikau, ta gwamnatin hadin gwiwan Austria, yace za a sake nazari a kan takardun izinin zaman kasar da aka baiwa limaman da kungiyar ATIB da take kula da masallatan Turkiya a can Austria, saboda wasu batutuwar kudade daga kasar waje.

Kickl ya ce sau biyu ana kwace takardun izinin zaman kasar a hannun limamai biyar da kuma hana wasu da suke neman izinin zaman a karon farko a cikin wannan lokaci.

Shugaban Austria Sebastian Kurz ya ce gwamnati zata rufe masallacin Turkiya na masu tsaurin ra’ayin addini a birnin Vienna kana a rusa kungiyar nan da take kiran kanta Arab Religious Community da take da masallatai shida.

Turkiya ta yi tur da wannan mataki da ta kira na nuna kiayayya ga musulunci da kuma wariyar launi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG