Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Iran Ta Yiwa Amurka Kashedi


Kasar Iran ta yiwa Amurka kashedin kada ta ayyana dogarawan juyin juya halin kasar a zaman kungiyar 'yan ta’ada, tana mai fadin cewa yin haka zai sa Amurka a bangare daya da kungiyar ISIS.

Yau Talata mai magana da yawun gwamnatin Iran Mohammed Bagher ya fadawa 'yan jarida cewa sojojin juyin juya hali, sojoji ne dake kare kasar Iran, kuma idan Amurka, ta ayyana wata rundunar soja a zaman kungiyar 'yan ta’ada, to ta sanya kanta cikin jerin ‘yan ta’ada.

Rahotanin kafofin yada labarun Amurka, sun bayyana cewa kila shugaba Donald Trump, na Amurka ya ayyana rundunar ta juyin juya hali a zaman kungiyar ‘yan ta’ada a zaman wani bangare na kara matsawa Iran lamba akan shirin nukiliyarta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG