Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun Yi Allah Wadai Da Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Afghanistan


Wadansu da suka ji rauni a harin Kabul
Wadansu da suka ji rauni a harin Kabul

Kasashen duniya sun bi sahun Amurka wajen yin Allah wadai da amfani da motar daukar marasa lafiya wajen kaiwa farin kaya hari a Afghanistan

Fadar White House ta fitar da sanarwa jiya asabar, tayin allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai jiya a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan da ya kashe mutane akalla 95 baya ga wasu 163 da su ka ji raunuka.

Tace wannan harin da ya janyo asarar rayuka, ya samu da abokiyar kawancenmu Afghanistan jajircewa. Muguntar Taliban ba zata dore ba. Amurka ta kuduri aniyar raba Afghanistan da 'yan ta'adda da zasu iya kaiwa Amurkawa da abokan kawancenmu da duk wanda baya ra'ayinsu hari.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ita ma ta fitar da sanarwa cewa, "Amfani da motar daukar marasa lafiya da kungiyar Taliban tayi a matsayi makami, ta kaiwa farin kaya hari, manuniya ce ta irin yadda bata dauki mutanen Afghanistan da duk wadanda suke kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar a matsayin komi ba, kuma wannan ya sabawa hankali. Muna jinjinawa dukan ma'aikatan gaggawa sabili da karfin halinsu wajen kai dauki bayan harin.

Shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan shima ya yi Allah wadai da harin yace abinda ya fi tada hankali da ya kuma sabawa dokar kasa da kasa shine yadda maharan suka yi amfani da motar da aka yiwa fenti kamar ta daukar marasa lafiya harda tambarin aikin jinya.

Makwabciya Pakistan da ake zargi da samarwa kungiyar Taliban mafaka ita ma ta yi Allah wadai da harin, ta kuma jajintawa dangin wadanda harin ya shafa.

An kai harin na jiya asabar ne, 'yan sa'oi bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa nakiya da aka dankare a wata karamar mota, a wajen sansanin soja dake lardin Helmand daku kudanci, inda ake fama da tashin hankali. Fashewar da ta auki a lardin Nad Ali ta jiwa a kalla dakarun gwamnati shida rauni, bisa ga cewar jami'ai.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG