Accessibility links

Kasashen Ketare Zasu Ba 'Yan Tawaye Karin Tallafi

  • Grace Alheri Abdu

Taron kasashen waje ma'abotan kasar Siriya
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry yace kasashen turai da kuma kasashen larabawa da suka raba gari da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad sun yi alkawarin kara tallafawa ‘yan tawayen Syria a wani taron da ake kira na ma’abotan Siriya da aka yi a Qatar jiya asabar.

Kerry ya bayyana cewa, ministocin kasashe goma sha daya sun yi alkawarin ba ‘yan tawaye karin tallafin soja da na ayyukan jinkai a yunkurin kawo karshen tashin hankalin tsawon shekaru biyu da ya yi sanadin kashe dubun dubatan Siriyawa.

Kerry yace, yayinda Amurka take kara tallafin da take ba ‘yan tawayen Siriya, hanyar da tafi dacewa da warware rikicin ita ce tattaunawa.
XS
SM
MD
LG