Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane 600 Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A India


Wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su a kasar Indiya

Kwararru sun ce yana yiwuwa a sake samun karin asarar rayuka sakamakon ruwa da ake ci gaba da tafkawa a arewacin kasar Indiya

Mummunan ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da aka yi a arewacin Indiya sun kashe kusan mutane dari shida yayinda dubun dubatan mutane kuma suka rasa inda zasu shiga da dama kuma suka bace.

Masu harsashen kan yanayi sun bayyana jiya asabar cewa, ana kyautata zaton ci gaba da tafka ruwa na tsawon kwanaki. Masu aikin ceto suna kokarin ceto sama da mutane dubu hamsin da ruwan ya datse a jihar Himalayan dake Uttarakhand, inda ruwan da aka rika tafkawa ya cinye kauyuka baki daya.

Masu aikin ceto rayuka sun ce sun taimakawa sama da mutane dubu talatin su isa wurin da zasu fake cikin kwanaki biyar da suka shige. Wadanda ambaliyar ruwan ya shafa sun hada da masu ayyukan ibada dake kan hanyarsu zuwa wuraren ibadar Hindi da kuma ‘yan yawon bude ido, wadanda sai da aka yi amfani da jirgi mai saukar angulu kafin a ceto su.

Kasar Indiya ta sha fuskantar ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, sai dai bana ruwan ya sauko mako guda kafin lokacin da aka yi harsashe, abinda ya sa mutane suka rika gudu suna neman mafaka a tuddai yayinda tekuna suka rika ambaliya.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG