Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA: Harkokin Kasuwanci a Tsohuwar Kasuwar Karamar Hukumar Yola Ta Arewa, Mayu 8, 2022


Yayin da ake hada-hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara “Tsohuwar Kasuwa” a karamar hukumar Yola ta arewa a jihar Adamawa, Najeriya.

Washington, DC - Wannan kasuwa dai na daga cikin kasuwannin da aka fara budewa a jihar Adamawa tun a lokacin da ta ke jihar Gongola. Ana saida tufafi, hatsi, kayan miya da sauran kayayyakin masarufi a cikinta.

Wakilin muryar Amurka Lado Salisu Garba, ya tattauna da ‘yan kasuwar da suka bayyana masa farashin kayayyaki a lokacin azumi, gabanin Sallah, da kuma a yanzu.

‘Yan kasuwar sun yi korafi game da rashin wutar lantarki da ke shafar sana’arsu, sun kuma bukaci gwamnati ta rage musu kudin wuta ta yadda zasu samu saukin harkokinsu.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:58 0:00

XS
SM
MD
LG