Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KEBBI: Iyalen Jami'an Tsaron Da Aka Kashe Sun Gudanar Da Zanga-zanga


Zanga-zanga
Zanga-zanga

A Najeriya iyalan jami'an tsaron da aka kashe a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar, sun gudanar da zanga zanga.

Mahukuntan jihar ta Kebbi sun ce a gudanar da addu'o'in neman jinkai ga jami'an da sauran wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar ayyukan ta'addanci.

Jami'an soji da ‘yan sanda goma sha tara ne ‘yan bindiga suka kashe a garin Kanya dake yankin masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Tun daga ranar da ‘yan bindiga suka hallaka jami'an soji da ‘yan sanda a wani harin kwantar bauna da suka yi wa mataimakin gwamnan jihar kebbi bayan sun kashe ‘yan sa kai fiye da 60, hankula suka karkata a jihar kebbi inda jama'a ke ta jajanta wa gwamnati da iyalan wadanda suka rasa rayukan su.

Sai dai wannan bai hana iyalan jami'an tsaron da aka hallaka ba, kai wa matuka ga damuwa da juyayi inda har wasu rahotanni ke nuna sun fusata sun gudanar da zanga zanga.

Wani hoton bidiyo na nuna mata su na zanga zanga dauke da kwalaye har da cinna wa tayoyi wuta don nuna damuwa.

Wani bidiyon kuwa ya nuna wani jami'in soja tare da wasu sojoji suna bayani ga matan domin kwantar ma su da hankali.

Wannan lamarin da ya faru a jihar kebbi abu ne na alhini ga kowa a cewar gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu.

Har wayau gwamnati ta umurci Musulmi da Kirista da su gudanar addu'o'in neman jinkai ga wadanda suka rasa rayukansu.

Jama'a dai na ci gaba da yin jaje da ta'aziyya ga gwamnati da iyalan wadanda hare haren ta’addancin su ka yi sanadin salwantar rayukansu, yayin da sauran jama'ar dake yankunan na kudancin Kebbi ke ci gaba da zaman dar-dar, inda tuni wasu su ka yi hijira zuwa manyan garuruwa don kauce wa abubuwan da ka iya faruwa.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da daidaita yankunan arewacin Najeriya tare da kassara jama'ar yankunan duk da kokarin da mahukumta ke cewa suna yi.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG