Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 70 Sun Nutse, 15 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-kwale A Jihar Kwara


Wani Hadarin Kwale-kwale a Sokoto
Wani Hadarin Kwale-kwale a Sokoto

Wani Mazaunin yankin da lamari ya faru Malam Muhammad Sani ya ce jirgin kwale-kwalen ya dauko wasu ‘yan biki ne daga kauyen Boti na yankin karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara.

KWARA, NIGERIA - Amma da suka je tsakiyar ruwan sai jirgin ya fashe. Malam Sani ya ce “ya zuwa yanzu an sami gawarwakin mutane 15 kuma ana ci gaba da neman sauran har yanzu’’

A lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi babbar jami’ar hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya - NEMA, mai Kula da jihohin Kwara da Neja, Hajiya Zainab Sa’idu ta ce ba ta riga ta samI labarin ba amma za ta tuntubi jami’anta da ke jihar ta Kwara.

Shugaban Karamar Hukumar Patigi Muhammad Ibrahim Liman ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce suna gudanar da bincike domin gano dalilin fashewar jirgin kwale-kwalen.

Idris Kpata Muhammad, sakataren karamar hukumar mulki ta Patigi ya ce lamarin ya tayar da hankalinsu matuka, amma kuma sun dauke shi a matsayin mukaddari ne daga Allah.

A baya an sha samun hadurran jiragen ruwan kwale-kwale a cikin kogunan Kwara da Neja da su ka yi sanadiyyar asarar rayuk kan jama’a, al’amarin da masu fashin baki suka ce yana bukatar daukar matakin shawo kan wannan matsala.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Kimanin Mutane 70 Suka Nutse, 15 Suka Mutu A Hatsarin Kwale-kwale A Gokin Jihar Kwara.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

XS
SM
MD
LG