Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Tsere A Kwale-kwale Daga ‘Yan Bindiga A Jihar Neja Sun Nutse A Teku


Hadarin Kwale Kwale 

Masu aikin ceto na can na neman wasu mutane da ba a tantance yawan su ba da wani jirgin ruwan kwale kwale ya kife dasu a jihar Neja.

NIGER, NIGERIA - Bayanai dai sun nuna cewa ‘yan bindiga ne suka auka a gari Shata ta yankin karamar hukumar Muya, al’amarin da ya sa mutanen garin suka shiga wannan jirgin kwale kwale domin neman tsira daga wadan nan ‘yan bindiga.

Amma kuma sai jirgin ya kife da su a tsakiyar ruwa. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya zuwa yanzu an samu gawarwaki na mutane 8.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sandan jihar Neja akan wannan al’amari, amma gwamnatin jihar ta tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

Alhaji Ibrahim Inga shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Nejan ya ce a hukumance sun samu labarin aukuwar lamarin kuma suna kan bincike.

A yanzu dai ana sa ran samun karin haske zuwa safiyar Alhamis din nan akan yawan mutanen dake cikin wannan jirgin ruwan kwale kwale.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Mutanen Da Suka Tsere A Kwale-kwale Daga ‘Yan Bindiga A Jihar Nejan Najeriya Sun Nutse A Cikin Ruwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG