Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristocin Najeriya Masu Zuwa Aikin Ziyara Sun Tashi Zuwa Jordan


Kiristocin Najeriya masu niyyar zuwa ziyara kasa mai tsarki
Kiristocin Najeriya masu niyyar zuwa ziyara kasa mai tsarki

Kiristocin Najeriya masu ziyara sun tashi a karon farko zuwa kasar Jordan don gudanar da ayyukan ibada tun bayan barkewar Annobar COVID-19.

Hukumar kula da masu ziyara zuwa kasa mai tsarki ta mabiya addinin Kirista ta ce masu ziyara 2,500 ne za su ziyarci kasar Urdun wato Jordan don duba wurare masu tsarki da gudanar da addu’o’i.

Mahajjata Kiristocin Najeriya
Mahajjata Kiristocin Najeriya

Shugaban hukumar ta kasa, Rev. Yakubu Pam ne ya bayyana hakan yayin da yake ban-kwana wa kashin farko na masu zuwa aikin ibadar daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato, karon farko tun bayan bullar cutar coronavirus a duniya.

Mahajjata Kiristocin Najeriya
Mahajjata Kiristocin Najeriya

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya ce gwamnati na daukar dawainiyar masu zuwa ayyukan ibadar ne don su je su gudanar da addu’oi ga kasa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Kiristocin Najeriya Masu Zuwa Aikin Ziyara Sun Tashi Zuwa Jordan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


XS
SM
MD
LG