Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Gilla Ga Tsohon Firmainistan Japan Shinzo Abe Akasin Bazata Ne Ga Duniya-Dr. Idi Hong


Shinzo Abe
Shinzo Abe

Kisan gilla ga tsohon firaministan Japan Shinzo Abe ya zo wa masu sharhi da mamaki a kasar da ta ke daukar tsauraran matakai kan amfani ko mallakar bindiga.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Dr. Idi Hong ya ce Japan na da rigimar siyasa amma ba ta kai wa ga zubar da jini irin wannan.

Shinzo Abe dai wanda ya zauna kan kujerar har tsawon shekaru 10 kafin sauka a bariya, ya cigaba da zama babbar fuska a siyasar Japan tamkar har yanzu ya na kan kujerar ne. Japan na daga kasashe da a ka fi samun masu kashe kan ma in sun yi wani abun kunya.

‘Yan sanda sun cafke wanda ya harbe shi ta baya mai suna Tetsuya Yamagami a wajen kamfen din zaben ‘yan majaliisa inda Yamagami ya ce bai gamsu da Abe ba ne don haka ya ke son kashe shi.

Tsohon ministan na wajen Njaeriya Dr. Idi Hong ya ce Abe ya yi ta amfani da hikimomi ne na kulla dangantaka har ya yi dogon zango kan mulki.

Masanin harkokin tsaro Dr. Yahuza Getso ya ce kisan gillar zai jawo sauran shugabanni musamman na kasashe masu tasowa kara karfafa tsaro a gewayen su, ya na mai kawo wasu dalilan rashin adalci kan tunzura jama’a su kangare.

Kasancewar wannan akasi ya zama ba sabam ba tun wajajen 1930, Dr. Hong ya ce Japan ta samu sabon darasi a tarihi.

Firaministan Japna mai ci Fumio Kishida ya nuna matukar takaicin aukuwar akasin ya na mai cewa sam ba za a yafe ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG