Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Ta Ce Ba Ta Da Sha'awar Tattaunawa - Tillerson


Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson

Korea ta Arewa ta ce ba ta da sha'awar hawan teburin tattaunawa da Amurka dangane da neman ta yi watsi da shirinta na mallakar makaman nukiliya, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce Korea ta arewa, ta nuna ba ta da sha’awar hawa teburin tattaunawa kan shirinta na mallakar makaman nukiliya.

A jiya Asabar Sakataren harkokin wajen kasar, Rex Tillerson ya tabbatar da cewa Amurka na ganawa kai-tsaye da hukumomin Pyongyang.

Tillerson ya kai ziyara a Beijing a jiya Asabar domin neman hadin kan kasar Sin wajen nuna matsin lamba ga kasar ta Korea ta arewa, inda ya tabbatar da cewa kasashen biyu suna tattaunawa.

Sakataren harkokin wajen Amurkan ya fadi cewa, sun bude kofar tattaunawa ta kai-tsaye da Korea ta arewa, tare da gudanar da bincike ko tana da kwadayin a hau teburin tattaunawa kan yin watsi da shirinta na mallakar makaman nukiliya.

A lokacin da aka tambayi Tillerson me suka tattauna da korea ta arewan sai, ya ce “mun tambaye su ne ko suna so a gana.”

Amurkan da Korea ta Arewan, kan tattaunawa ne ta hanyar shiga tsakanin da wasu kasashe ko tsoffin jami’ai ke yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG