Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koria Ta Kudu: An Yanke Wa Choi Soon-Sil Hukuncin Daurin Shekaru 62


Kotu a kasar Koria ta kudu ta yankewa Choi Soon-Sil, kawar tsohuwar shugabar kasar hukuncin daurin shekaru 62, da tarar kudi sama da dalar Amurka miliyan $17, a sakamakon bankado badakalar cin hanci da rashawa, lamarin da ya yi sanadiyyar faduwar shugabar daga karagar mulki.

An yankewa matar da kawancenta da tsohuwar shugabar kasar Korea ta Kudu, Park Geun-hye ya haifar da badakalar cinhanci da rashawa da ta yi sanadiyyar faduwarta daga mulki, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso.

A yau Talata ne aka yankewa Choi Soon-Sil, hukunci a wata kotu dake Seoul, akan cin hanci da rashawa da amfani da iko da ya wuce kima, da katsalandan a harkokin gwamnati. Kotun kuma ta saka mata tara mai tsanani ta kusan kudi dalar Amurka miliyan $17.

Ba laifin anfani da iko kadai ba, an kuma zargi matar mai shekaru 62 da haihuwa, da laifin zama wata mai yawan tasiri akan tsohuwar shugaba Park, har ta zama kamar “wadda take bautawa” duk da cewa bata da wani mukami na musamman a gwamnati.

Amma ta yi amfani da alakar dake tsakaninta da tsohuwar shugabar wajan tilasatawa manyan kamfanoni bada gudummuwar kudi sama da dalar Amurka miliyan $68 ga wata kungiya mai zaman kanta da take jagoranta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG