Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Gidajen Talibijin A Amurka Sun Juyawa Shugaba Trump Baya


Donald Trump
Donald Trump

Wasu Gidajen Talibijin A Amurka Sun Ki Nuna Tallar Nasarorin Shugaba Trump

Gidaje talibijin da dama anan Amirka da suka hada harda ABC da CBS da NBC da kuma CNN sun ki su nuna talar irin nasarori da shugaba Donald Trump yace ya samu cikin kwanaki dari da yayi yana jan ragamar mulki.

Talar ta kunshi ma’aikatan gidan talibijin da alamar labaran karya akan fuskokin su.

Galibi duk wani labari ko rahoto daya caccaki manufar shugaba Donald Trump, shi a wurin sa labari ne ko kuma rahoto ne na karya.

Gidajen talibijin sun hakake akan cewa ba kashin gaskiya a talar. Gidajen talibijin na CNN da NBC sun ce zasu nuna talar idan aka fitar da rubutun da aka yi dake cewa labarai ko kuma rahotanin karya a fuskokin ma’aikatan su.

Kwamitin yakin neman zaben shugaba Trump ne ya hada talar. Tuni har shugaba Trump yace zai nemi a sake

zabensa shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da ashirin idan Allah ya kaimu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG