Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Zata Kwance Makaman Nukiyarta Cikin Shekara Biyu Da Rabi - Pompeo


Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Amurka

Yayinda sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke ikirarin cewa Koriya ta Arewa zata kwance makaman nukiliyarta nan da zuwa shekara biyu da rabi su kuwa 'yan Democrat na ganin akwai jan aiki gaba kafin duniya ta samu masalaha.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce suna sa ran nan da shekara biyu da rabi, Koriya ta Arewa za ta kwance damarar makamanta na nukiliya da gasken-gaske.

Kalaman na Pompeo wadanda ya yi a jiya Laraba, na zuwa ne, kwana guda bayan da shugaba Donald Trump ya rattaba hannu akan wata yarjejeniya da shugaban Koriya ta Arewan, Kim Jong Un, wacce ta nemi a kawo karshen shirin makaman nukiliyan na kasar.

Sai dai a cewar ‘yar majalisar Dattawa a bangaren ‘yan Democrat, Sanata Jeanne Shaheen, akwai sauran jan aiki a gaba kafin duniya ta numfasa dangane da makamin nukiliyan na Koriya ta Arewa.

ACT 1 “Wannan barazanar nukiliya ba za ta kau ba, har sai sun wargaza baki dayan cibiyar makamin nukiliyan, su kawar da fasahar bunkasa makamin baki dayansa.”

Shi kuwa Sanata John Cornyn na bangaren ‘yan Republican, ya fadawa Muryar Amurka cewa, duk da wannan taron kolin da aka yi a Singapore, babu abin da zai canza dangane da matsalin lambar da ake nunawa hukumomin Pyongyang.

ACT 2 “Fassarar da na yi wa wannan taro na su na farko, wanda ya zo wa kowa da mamaki, ita ce, kamar ‘yan dambe ne biyu, suka yi musabaha gabanin sun fara dambatawa, ba’a a fara ainihin tattaunawar ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG